UAE ta kawo ƙarshen dokar hana ƴan Najeriya biza bayan Tinubu ya kai ziyara Abu Dhabi

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi nasarar kulla wata yarjejeniya mai cike da tarihi tsakanin Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), wanda ya kawo karshen dokar hana bizar da ta yi wa ƴan Najeriya.

An samu nasarar ne a ziyarar da shugaba Tinubu ya kai Abu Dhabi, bayan halartar taron kasashen G-20 da ya gudana a kasar Indiya.

Muhimmin abin ya faru ne lokacin da Ambasada Designate, Amb Salem Saeed Al-Shamsi, ya gabatar da wasiƙarsa ga shugaba Tinubu a Aso Rock, Nijeriya.

Shugaban kasar bai bata lokaci ba wajen jagorantar warware takaddamar diflomasiyya da ta dade tana wanzuwa.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Cif Ajuri Ngelale, ya bayyana cikakken bayanin yarjejeniyar a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, yana mai bayyana ganawar da mahukuntan UAE a matsayin mai matukar fa’ida.

More from this stream

Recomended