Tsohon shugaban kungiyar ƙwadago ta NLC, Ali Chiroma ya rasu.
Ibrahim Chiroma ɗan uwa ga marigayin kuma sakataren kungiyar ƴan jaridu ta NLC shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri.
Ya ce tsohon shugaban ƙungiyar ƙwadagon ya rasu a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri kuma anyi jana’izarsa ranar Laraba a Maiduguri.
Chiroma ya jagoranci kungiyar ta NLC daga shekarar 1984 zuwa 1988 lokacin da shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya rushe ƙungiyar.
A shekarar 1993 tsohon shugaban ƙasa, Janar Sani Abacha ya na ɗashi shugaban ƙungiyar NUPENG.