Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Borno, Alhaji Usman Jidda Shuwa ya riga mu gidan gaskiya.
Shuwa wanda har ranar 29 ga watan Mayu shi ne sakataren gwamnatin jihar ta Babagana Umara Zulum ya mutu bayan gajeriyar rashin lafiya.
A cewar wata majiya dake iyalan mamacin ya mutu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.
Shuwa kwararren ma’aikacin gwamnatin ne da ya yi aiki a gwamnatin tarayya da kuma ta jiha.
Ya rasu yana da shekaru 65.