Tsohon gwamnan Adamawa ya fice daga jam’iyyar APC

Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow ya fice daga jam’iyyar APC.

Fitarsa daga jam’iyyar na kunshe ne cikin wata takarda da ya aikewa shugaban jam’iyyar APC na mazabar Kolere dake karamar hukumar Mubi North.

Bindow ya ayyana dalilansa na barin jam’iyar da suka hada rashin sasanta rikicin jam’iyyar tun daga 2019 har kawo yanzu da aka samu rikici biyo bayan zaben fidda gwani.

Ya ce matakin da ya dauka na ficewa daga jam’iyyar ba abu ne mai sauki kuma ya dauke shi ne bayan mika komai ga Allah tare da tuntubar magoya bayansa a dukkan sassan jihar baki ɗaya.

More from this stream

Recomended