Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin dimokuradiyyar a Najeriya.
Wannan adadin ya samo asali ne daga zargin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta yi wa tsofaffin Gwamnonin.
Adadin naira tiriliyan 2.187 bai hada da kadarorin da aka kwace da kuma wasu da ake bincike a kai na biliyoyin naira ba.
A cewar jaridar Vanguard, kudaden da aka wawashe dai sun yi daidai da kasafin kudin jihar Legas na shekarar 2024 (N2.25 trillion) da daukacin jihohin kudu maso gabas (N2.29 trillion).