
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
A karshen shekarar da ta gabata ne cutar korona ta bulla, amma alamomi sun bayyana da ke nuna cewa ana iya daukar lokaci mai tsawo kafin wadanda suka kamu su sami cikakkaiyar lafiya.
Samun sauki zai dogara da irin kamun da cutar ta yi wa mutum. Wasu na iya warkewa nan da nan, amma ga wasu cutar na iya zama sanadiyyar wasu cutukan masu dorewa.
Shekaru da jinsi da sauran cutuka a jikin mutum na iya kara zama barazana idan mutum ya kamu da cutar.
Idan aka bai wa mutum kulawa ta musamman, kuma idan aka dade yana samun wannan kulawa, zai dade bai warke garau ba.
Idan cutar bata yi min mugun kamu ba fa?
Mutane da yawa da za su kamu da cutar korona, za su samu manyan alamominta ne kawai – tari da zazzabi. Amma za su iya samun ciwon jiki da mutuwar jiki ko gajiya da ciwon wuya da ciwon kai.
Tarin yakan fara ne ba tare da majina ba, amma ga wasu yana iya zama mai majina wacce take dauke da matattun kwayoyin halitta na cikin huhu da kwayar cutar ta kashe.
Wadannan alamomin na yin sauki idan aka samu hutu tare da shan ruwa sosai da shan magungunan rage radadi kamar paracetamol.
Mutanen da alamomin cutar ba su bayyana a jikinsu sosai ba na saurin samun sauki.
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Zazzabin na tafiya bayan ‘yan kwanaki, amma tarin na iya dan dadewa.
Wani binciken Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, kan alkaluman China na cutar ya ce a kan dauki mako biyu a warke daga cutar.
Idan alamomin cutar sun bayyana sosai a jikina fa?
Cutar na iya kama wasu sosai fiye da wasu. Wannan kan faru ne kwanaki bakwai zuwa 10 bayan cutar ta shiga jikin mutum.
Kuma cikin lokaci kankani alamomin suke rikida. Numfashi zai fara sarkewa kuma huhu ya kumbura.
Haka na faruwa ne saboda, duk da cewa garkuwar jiki na kokarin yaki da cutar – tana aiki tukuru ne kuma wannan na rage mata karfi.
Cutar kan kama wasu sosai har sai an kai su asibiti an shaka masu iskar oxygen.
Wata Likita sarah Jarvis ta ce: “Ana iya dadewa sarkewar numfashi ba ta gyaru ba… jikin mutum na kokarin farfadowa daga kumburin nan da wahalar da ya sha.”
Ta ce ana iya daukar makonni biyu zuwa takwas kafin a warke, kuma ko bayan an warke a kan ci gaba da jin gajiya a jiki.
Idan ina bukatar kulawa ta musamman fa?
WHO ta yi kiyasin cewa mutum daya cikin mutum 20 za su bukaci a ba su kulawa ta musamman, wanda ka iya zama yi wa mutane allurar bacci sannan a hada masu na’urar shakar iska ta ventilator.
Ana daukar lokaci mai tsawo kafin a warke garau idan har aka kwantar da mutum a dakin bayar da kulawa ta musamman (ICU), dalilin wata irin cuta.
A kan mayar da marasa lafiya dakunan kwantar da marasa lafiya na yau da kullum kafin a sallame su su tafi gida.
Dakta Alison Pittard, Shugabar Tsangayar Bangaren Kulawa ta Musamman, ta ce ana iya daukar watanni 12 zuwa 18 kafin wanda ya kwanta a dakin kulawar gaggawa ya warke garau.
Dadewa a kwance a asibiti na haifar da rama. Marasa lafiya za su rasa karfin jikinsu kuma za su dade ba su mayar da kibarsu ba. Wasu ma kan bukaci taimako na musamman kafin su iya sake tafiya.
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Cibiyar bai wa masu cutar korona taimako na musamman a Faransa
Saboda irin gwagwarmayar da jiki ya sha a dakin na kulawa ta musamman, akwai kuma yiwuwar kamuwa da cutukan kwakwalwa.
“Akwai wani abu na daban dangane da wannan cuta – mutuwar jiki dalilin cutukan virus na taka muhimmiyar rawa,” in ji Paul Twose, mai ba da kulawa ta musamman a bangaren motsa jiki a cibiyar Lafiya ta Jami’ar Cardiff da Vale.
An samu mutane a China da Italiya da ke cewa suna fama da rashin karfin jiki, daukewar numfashi bayan sun yi aikin da bai kai ya kawo ba, da kuma tarin da ya ki ci ya ki cinyewa da daukewar numfashi da bukatar bacci sosai.
“Amma mun san cewa marasa lafiya na daukar lokaci mai tsawo, wani lokaci watanni kafin su samu sauki.”
Amma ba kowa ne ke fuskantar haka ba. Wasu ba sa dadewa a dakin kulawa ta musamman, yayin da wasu kan dauki makonni suna amfani da na’urar iska ta ventilator.
Shin cutar korona za ta shafi lafiyata daga baya na tsawon lokaci?
Ba mu da tabbas a kan wannan saboda babu alkaluma, amma muna iya duba wasu cutukan.
Cutukan sarkewar numfashi da ake kira ARDS na kama wadanda garkuwar jikinsu ta dade tana aiki tukuru, wannan na janyo huhu ya lalace.
“Akwai bayanai masu kyau da ke nuna cewa, ko nan da shekara biyar, mutane na iya ci gaba da fuskantar matsaloli a jikinsu,” in ji Mista Twose.
Dakta James Gill, wani likita kuma malami a jami’ar Warwick ya ce mutane na bukatar a kula da lafiyar kwakwalwarsu don taimaka masu wurin samun sauki.
“Numfashinka na sarkewa, sai likita ya ce maka ‘za mu sa maka na’urar iska. Za mu yi maka allurar bacci. Za ka yi sallama da iyalinka?’
“Ba abin mamaki ba ne idan wadannan marasa lafiyan suka kamu da cutar tsananin damuwa dalilin abubuwan da suka fuskanta a lokacin da ba su da lafiya.”
Haka kuma, akwai yiwuwar cewa marasa lafiyar da cutar ba ta kama su sosai ba na iya fuskantar matsaloli daga baya kamar yawan gajiya.
Mutane nawa ne suka warke daga cutar?
Samun sahihan alkaluma zai yi wuya.
Zuwa ranar 15 ga watan Afrilu, Jami’ar Johns Hopkins ta ruwaito cewa kusan mutum 500,000 ne suka warke daga cikin mutum miliyan biyu da suka kamu da cutar.
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Wani da ya warke daga cutar korona a Moroko yana sujjada bayan an sallame shi daga asibiti
Amma kasashe na amfani da hanyoyi da yawa na tattara alkalumanta. Wasu ba sa fitar da alkaluman mutanen da suka warke kuma akwai wadanda cutar ba ta kama sosai ba, don haka ana iya yin kuskure.
Wasu tsare-tsaren gwaji sun yi kiyasin cewa kusan kashi 99 zuwa 99.5 cikin dari na mutane na warkewa daga cutar.
Zan iya sake kamuwa da cutar Covid-19?
An ta ce-ce-ku-ce, ba tare da shaida ba, kan kariyar da garkuwar jiki ke da ita.
Idan masu dauke da cutar suka warke, hakan na nufin garkuwar jikinsu ta zama daki bari dangane da cutar.
Rahotannin da ke nuna cewa akwai mutanen da suka kamu da cutar sau biyu, na iya nufin ba a yi gwajin daidai ba.
Batun garkuwar jiki na da muhimmanci don fahimtar yadda mutane ke iya kara kamuwa da cutar da kuma yadda riga kafi ka iya tasiri kan cutar.
Kuna iya bin James on Twitter