
Asalin hoton, Getty Images
Tsawa ta kashe yara 10 a garin Arua da ke arewa maso yammacin Uganda. An kwana biyu ana zabga ruwan sama a yankin tare da walƙiya da tsawa.
Ruwan da aka yi mai ƙarfi a ranar Alhamis ya ja yaran suka bar ƙwallon ƙafar da suke bugawa domin rakuɓewa ƙarƙashin wata bukka.
Ana cikin ruwan ne sai tsawa ta faɗa kan bukkar. Yara tara da ke tsakanin shekara 13 zuwa 15 suka mutu nan take, sai kuma ɗayan yaron ya mutu a hanyar kai shi asibiti.
Yara uku da suka tsira na jinya a wani asibiti da ke yankin.
Yankin arewacin Uganda na fama da ruwan sama kamar da bakin-ƙwarya da ke tafe da tsawa da walƙiya.
Makamancin wannan lamarin shi ne ma fi muni da ya faru a Uganda tun bayan makamancin hakan da ya faru a 2011, lokacin da yara 18 suka mutu a lokacin daukan darrusa a makaranta.
A wannan shekarar, mutum 28 sun sake mutuwa bayan sake wata tsawar duk a cikin mako guda.