‘Tsananin damuwa ke sa soja ya kashe kansa’

Rundunar soji
Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wani masanin tsaro a Najeriya Group Captain Sadik Garba Shehu ya ce matsalar da ke sa wasu sojoji kashe kansu da kansu ba ya rasa nasaba da halin da sojojin ke shiga musamman wadanda suke fagen fama.

Group Captain Shehu ya bayyana haka ne a hirarsa da BBC sa’o’i bayan da rundunar sojin Najeriya ta fitar da wata sanarwa cewa wani soja da ke aiki da Rundunar Lafiya Dole wacce ke yaki da Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, ya kashe abokan aikinsa hudu, sannan ya harbe kansa.

Masanin ya ce sojojin da ke fagen fama na ganin abubuwan tashin hankali – ko an kashe abokan aikinsa ko tunanin iyalinsu ko an kashe mutane, wanda hakan yake taba hankalinsu har ma su shiga tunane-tunane.

Ya ce akwai sojojin da irin tashe-tashen hankulan ba ya sa su tunani sai dai akwai wadanda suke shiga yanayin tunani da zai samu cutar damuwa ta Post Traumatic Stress Disorder.

“Idan cutar ta yi nisa za ta mutum ya rika tunanin kashe kansa ko wani” in ji masanin.

Ya kara da cewa ko da sojan ba ya fagen yaki, abubuwan da ya gani na tashin hankali a lokacin da yake yaki zai sa ya rika tunani har ya shiga damuwa.

Ya ce akwai abubuwan da ya kamata hukumomi da sojoji da kuma iyalansu ya kamata su yi domin kare afkuwar irin haka.

A cewarsa, kamata ya yi gwamnati ta samu masana su rika yi wa sojojin da za su je fagen fama bayani kan banbancin zama a fagen fama da kuma zaman gida, “su tabbatar cewa sojoji sun fahimci wannan.”

A bangaren soja, “idan ya ji yana da damuwa, kamata ya yi ya samu likitansa ko na gaba da shi domin sanar da shi halin da yake ciki.”

“Su kuma iyalan sojoji idan mutum ya dawo daga yaki aka ga halayyarsa ta canja, ko da mai magana ne amma ba ya magana da mutane ko kuma yana tashi ba ya barci ko yana yawan razana, sai ka kai gaba,” a cewarsa.

Ya kara da cewa kowane soja ya san da hadarurrukan da ke tattare da aikin soja kuma a ganinsa, hakan ba zai kashe wa soja gwiwar ka da ya shiga aikin ba saboda kowane aiki yana da nasa hadarin.

A ganinsa, irin wannan abu zai sa gwamnati ta tabbatar cewa masu irin wannan matsalar an samu masana sun ba su shawara saboda a dakile kai wa ga matakin kisan kai.

Ya ce lamarin ba zai kawo illa ga yakin da ake da Boko Haram ba “abin da zai kawo illa shi ne idan mutane suka san cewa ba a ba wa sojoji taimako a kai.”

“Amma idan kasan kana da matsalar iyalinka suka san za a taimaka maka,” ba za a samu wata illa ba, in ji shi.

Ya ce babban abin da zai kawo matsala shi ne “barin soja ya je ya ji da wahalarsa ba a taimaka masa ba”.

Matakan kariya a takaice

  • Yi musu bayani kan banbancin zama a fagen fama da kuma zaman gida
  • Ganin likita a lokacin da ya ji yana da damuwa don sanar da halin da yake cikir
  • Daukar mataki idan aka fahimci halayyar mutum ta sauya
  • A hada su da masana su dinga ba su shawara
  • A dinga taimaka wa sojojin a inda ya dace musamman wajen magance matsalolinsu.

More from this stream

Recomended