
Rikicin da ya dabaibaye jam’iyar PDP ya dauki wani sabon salo a ranar lokacin da wani tsagin jam’iyar dake biyayya ga tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike su ka kwace ikon ginin hedkwatar jam’iyar dake Wadata Plaza a Abuja.
Ana tsaka da rikicin ne ɓangaren Wike ya nada, Muhammad Abdulrahaman a matsayin shugaban jam’iyar na riko bayan da suka dakatar da shugaban jam’iyar, Umar Damagum.
Tun da farko kafin a kawo halin da ake ciki yanzu sai da shugabancin jam’iyar karkashin jagorancin, Damagum ya dakatar da Samuel Anyanwu da kuma wasu shugabannin jam’iyar dake biyayya ga Wike.
Da yake wa yan jaridu jawabi a Abuja sabon shugaban jam’iyar ta PDP tsagin Wike ya ce kudirinsa shi ne haɗakan jam’iyar.
Shugaban ya gudanar da wata ganawa a hedkwatar jam’iyar tare da Anyanwu da kuma wasu shugabanni da suka fito daga tsagin na Wike.

                                    