Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa sun kama wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne.
Mataimakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Abubakar Isah, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Dutse, babban birnin jihar.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar 12 ga Disambar 2023, a jihar Kano.
Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin a matsayin Yusuf Yusuf dan shekara 25 daga unguwar Katoge da ke karamar hukumar Kazaure da kuma Umar Abubakar mai shekaru 23 daga kauyen Dakayyawa a karamar hukumar Kaugama.