
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai halarci taron ƙasar Saudiya da kasashen Afrika da kuma taron kasashen Larabawa da na Afrika da za ayi a birnin Riyadh na kasar Saudiya.
Tarukan biyu za a gudanar da su ranar 10 da 11 ga watan Nuwamba.
A wata sanarwa ranar Lahadi, Ajuri Ngelale mai magana da yawun shugaban ƙasa ya ce Tinubu zai halarci taron a wani bangare na ƙoƙarin da yake na samun karin kwararowar kuɗade wajen cikin tattalin arzikin Najeriya.
Ya ce Tinubu zai jagoranci ƙoƙarin da Afrika take na amfana daga yarjejeniyar AFCTA ta kasuwancin bai ɗaya a nahiyar.
A taron za a tattauna batutuwa da dama kan tattalin arziki da suka shafi nahiyoyin biyu.