Tinubu zai halarci bikin rantsar da shugaban ƙasar Chadi

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu zai halarci bikin rantsar da shugaban ƙasar Chad, Mahamat Deby.

A wata sanarwa da Ajuri Ngelale mai magana da yawun shugaban ƙasar ya fitar ranar Laraba ya ce Tinubu zai ta shi daga Abuja ya zuwa N’Djamena babban birnin ƙasar Chad a ranar Alhamis kuma zai dawo bayan kammala bikin.

Deby wanda ya kasance shugaban riƙo na kasar an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 6 ga watan Mayu bayan da majalisar tsarin mulki ƙasar ta tabbatar da shi.

Majalisar ta ayyana Deby a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan da tayi watsi da ƙorafin ƴan takarar shugaban ƙasa biyu Success Masara da kuma Albert Padacke.

Ngelale ya ce Tinubu zai samu rakiyar manyan jami’an gwamnati.

More from this stream

Recomended