
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Bola Ahmad Tinubu zai jagoranci taron shugabannin kungiyar ECOWAS a Abuja kan juyin mulkin kwanannan da aka yi a Jamhuriyar Nijar.
Mai bawa shugaban kasa shawara kan sadarwa, Dele Alake shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
A daren ranar Laraba ne, Kanal Amadou Abdramane ya sanar da sauke shugaban kasa, Mohamed Bazoum daga kan kujerarsa.
Taron na ranar Lahad 30 ga watan Yuli zai gudana ne a Abuja.