Tinubu Ya Yi Alƙawarin Nemo Karin Hanyoyin Murƙushe Rashin Tsaro

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na nemo hanyoyin da za su kawo ƙarshen ta’addanci da ayyukan ’yan bindiga a ƙasar nan.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin jawabin buɗe taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (NEC) kan bunƙasa tattalin arziƙi mai haɗa kai da ci gaban ƙasa mai ɗorewa, wanda ke gudana a Abuja.

Shugaban ya kuma yaba wa wasu gwamnonin jihohi, musamman na Borno, Katsina da Kaduna, bisa rawar da suke takawa wajen kare ’yanci da tsaron ƙasa.

More from this stream

Recomended