Tinubu Ya Tafi Ziyarar Aiki Ƙasashen Turai

Zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bar Najeriya a ranar Laraba ya zuwa ƙasashen turai inda zai fara ziyarar aiki ta wasu yan kwanaki.

A cikin wata sanarwa mai ɗauke da sahannun Tunde Rahman jami’in dake magana da yawun ofishin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya ce Tinubu zai amfani da ziyarar wajen tsara manufofi da kuma tsare-tsaren da gwamnatinsa za ta zo da su.

Har ila yau zai yi amfani da ziyarar wajen jawo hankalin masu zuba jari a Najeriya.

Wannan ne dai karo na biyu da Tinubu yake kai ziyara ƙasashen Turai tun bayan da aka bayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen shugaban kasar Najeriya.

More from this stream

Recomended