Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu zai tafi ƙasar Faransa a ranar Laraba a wata ziyara da zai kai ta ƙashin kansa.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ta ce Tinubu zai gana da shugaban kasar,Faransa Emmanuel Macron a yayin ziyarar.
Onanuga ya ce daga bisani shugaban ƙasar zai wuce Addis Ababa babban birnin kasar Habasha.
A Habasha Tinubu zai halarci taron shugabannin ƙasashen kungiyar Tarayyar Afirka da za a gudanar daga ranar 12 zuwa 16 ga watan Fabrairu.
A watan Nuwamban shekarar da ta wuce Tinubu ya kai ziyarar aiki ƙasar ta Faransa inda ya gana da shugaban kasa, Emmanuel Macron.