Tinubu ya sanar da ƙarin albashin dubu 25 ga ƙananan ma’aikata

Shugaba Bola Tinubu ya sanar da karin albashi na wucin gadi na watanni shida ga wasu ma’aikata a kasar.

Shugaban kasar ya sanar da karin ne a jawabinsa na bikin cikar ‘yancin kai na farko a ranar Lahadi.

Karin albashin dai shi ne zai taimaka wajen dakile radadin cire tallafin man fetur, wanda ya haifar da tsadar rayuwa a kasar.

“Bisa tattaunawar da muka yi da ma’aikata, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, muna bullo da karin albashin na wucin gadi domin inganta mafi karancin albashi na tarayya ba tare da haifar da hauhawar farashin kayayyaki ba,” in ji Tinubu.

“Na tsawon watanni shida masu zuwa, matsakaitan ma’aikata za su rika samun karin Naira Dubu Ashirin da Biyar a kowane wata.”

More News

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...

Sojojin Najeriya Sun Musanta Jita-jitar Mutuwar Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja

Daga Sabiu AbdullahiRundunar Sojojin Najeriya ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja,...