Tinubu ya sake naɗa Mele Kyari a matsayin shugaban NNPCL

Shugaba Bola Tinubu ya sake nada Malam Mele Kyari a matsayin babban jami’in gudanarwa na kamfanin man fetur na kasa (NNPCL).

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Litinin.

A cewar Ngelale, nadin zai fara aiki ne daga ranar Juma’a 1 ga Disamba, 2023.

Ya ce shugaban ya kuma nada kwamitin gudanarwa na kamfanin, tare da Cif Pius Akinyelure a matsayin shugaban hukumar da ba na zartarwa ba.

More from this stream

Recomended