
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya rantsar da Bernard Doro da Kingsley Udeh a matsayin ministoci a majalisar zartarwa ta tarayya a yayin wani gajeren biki da aka yi a fadar Ado Rock.
Bikin ya gudana ne jim kadan kafin zaman majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban kasa Tinubu ya jagoranta a ranar Alhamis.
Doro wanda ya fito daga jihar Filato ya maye gurbin, Nentawe Yilwatda ministan ma’aikatar jin kai da yaki da talauci wanda ya yi murabus domin zama shugaban jam’iyar APC, a cikin watan Oktoba ne majalisar dattawa ta tantance tare da amincewa da Doro a matsayin minista.
Udeh ya maye gurbin, Uche Nnaji a matsayin ministan kimiya da fasaha wanda ya yi murabus sakamakon zargin takardun karatu na jabu.
A ranar Alhamis ne majalisar dattawa ta tantance Udeh tare da tabbatar da shi a matsayin minista bayan wata yar gajeriyar tantancewa.
Kafin ya zama minista Udeh ya rike muÆ™amin kwamishinan shari’a na jihar Enugu.

