Tinubu ya nemi Yarima ya yi sulhunta gwamna Dauda Dare da Matawale

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yariman Bakura ya ce shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya nemi da ya jagoranci sulhu tsakanin gwamna Dauda Lawal Dare da kuma tsohon gwamna Bello Matawalle.

Yarima ya bayyana haka ne lokacin d yake ganawa da yan jaridar dake fadar shugaban kasa bayan da ya gana da Tinubu.

Da aka tambaye shi mai yake yi a matsayin sa na uba a jihar Yarima ya kada baki ya ce akwai shirin da ake na sasanta rikicin dake tsakanin mutanen biyu.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa a tattaunawar ta su shugaban kasar ya ce ya yi iyakacin iyawararsa wajen kawo karshen rikicin.

Har ila yau Yarima ya yabawa Tinubu kan cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi

More from this stream

Recomended