Tinubu ya naÉ—a sabon gwamnan CBN

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya naÉ—a Dr. Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) na tsawon shekara biyar.

Naɗin nasa zai fara aiki ne da zarar Majalisar Dattijan ƙasar ta amince da shi.

Wannan bayani na Æ™unshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Æ™asar, Ajuri Ngelale ya fitar, yau Juma’a.

Bayanin ya ce shugaban ƙasar ya ɗauki matakin ne bisa dogaro da sashe na 8 (1) na dokar Babban Bankin Najeriya ta 2007, wadda ta bai wa shugaban ƙasar karfin ikon naɗa shugaba da mataimaka huɗu na Babban Bankin.

Sanarwar ta kuma bayyana sunayen wasu mutane huÉ—u da shugaban ya amince da su domin naÉ—awa a matsayin mataimakan gwamnan babban bankin na Najeriya.

More News

An kuÉ“utar da wasu É—aliban da aka sace a jami’a a Kogi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta bayyana cewa an ceto 14 daga cikin daliban jami’ar kimiyya da fasaha ta Confluence da ke Osara Okene...

Hukumar NMDPRA ta rufe wani gidan mai da ya karkatar da tankar man fetur 18

Hukumar NMDPRA dake lura da tacewa tare rarraba man fetur da iskar gas ta rufe gidan man Botoson Oil and Gas LTD dake jihar...

Jirgin saman kamfanin Xejet ya zame daga kan titin filin jirgin saman Lagos

A ranar Asabar ne wani jirgin sama mallakin kamfanin Xejet ya zame daga kan titin filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos. Hukumar NSIB dake...

Lauya ya nemi kotu ta bashi mako 4 ya nemo inda Yahaya Bello ya É“uya

Abdulwahab Mohammed babban lauyan tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya nemi babbar kotun tarayya dake Abuja da ta bashi makonni huÉ—u domin ya...