Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya naɗa kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Ibrahim Hassan Hadejia shi ne zai kasance mataimakin shugaban ma’aikatan fadar ta shugaban kasa.
Har ila yau Tinubu ya naɗa tsohon gwamnan jihar Benue, George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
Wannan ne naɗe-naɗe na farko da shugaban kasar ya fara yi tun bayan da aka rantsar da shi a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.