Tinubu ya mayar da hedikwatar kula da filayen jirgin sama daga Abuja zuwa Legas

Gwamnatin tarayya ta mayar da hedikwatar hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya zuwa Legas daga Abuja.

Hakan ya fito ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Manajan Daraktar FAAN, Mrs Olubunmi Kuku.

Takardar cewa ta yi: “Mai girma ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya ya bayar da umarnin mayar da hedikwatar hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa (FAAN) daga Abuja zuwa Legas.

“Saboda wannan, ana buƙatar ku fara tattarawar zuwa sabon wurin.”

More from this stream

Recomended