Tinubu ya kai ziyara Maiduguri

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya isa Maiduguri domin jajantawa al’umma da gwamnatin jihar Borno kan ambaliyar ruwa da ta faru a jihar.

A ranar 10 ga watan Satumba ne ambaliyar ta raba dubban mutane daga gidajensu a yankunan Fori, Galtimari, Gwange, da kuma  Bulabulin dake  Maiduguri.

Mutanen da basu gaza 30 ba ne aka tabbatar da sun mutu a ambaliyar da ta faru sanadiyar ɓallewar madatsar ruwa ta Alou dake Maiduguri.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ziyarci birnin sa’o’i ƙadan bayan ambaliyar ruwan da ya ayyana ta mafi muni da ta faɗawa  jihar a cikin shekaru 30.

Da yake magana a lokacin ziyarar Shettima ya ce ɓarnar da ambaliyar ruwan tayi baza ta misaltu ba.

Tinubu ya bada umarnin gaggauta ɗauke mutanen da abun ya shafa a kuma sama musu matsuguni.

More from this stream

Recomended