Tinubu ya kai wa Osinbajo ziyarar ba zata a fadarsa

Dan takarar shugabancin Najeriya a APC, Bola Tinubu, ya kai wa Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, ziyara a fadar shugaban kasar da ke Abuja a daren Alhamis.

Bayan tattaunawa da Osinbajo, ya kuma ziyarci shugaba Muhammadu Buhari.

Tinubu ya samu kuri’u 1,271 a zaben fitar da gwanin APC, inda ya doke sauran ‘yan takara ciki har da Osinbajo wanda ya samu kuri’u 235.

Ziyarar Tinubu na zuwa ne bayan Mista Osinbajo ya mika sakon taya murna ga Tinubu da nuna mubaya’ar aiki tare da shi domin nasara a babban zabe.

More from this stream

Recomended