Tinubu Ya Kaddamar da Motocin Gas da Wutar Lantarki guda 107 a Borno

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da motoci masu aiki da gas da wutar lantarki guda 107 a birnin Maiduguri na Jihar Borno

Da yake jawabi a wajen bikin, Shugaban ya yaba wa Gwamna Babagana Zulum bisa hangen nesa da kuma tsare-tsare da ayyuka na inganta rayuwar mutane.

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta shirya kafa wata masana’anta ta wannan hanya domin samar da ayyukan yi da kuma saukaka harkokin sufuri.

Tun da farko, Zulum ya ce ya fara aikin ne biyo bayan umarnin da shugaban kasa ya ba gwamnoni bayan cire tallafin mai.

Ya ce tura motocin haya guda 50 masu amfani da wutar lantarki shi ne irinsa na farko a Najeriya kuma ya yi daidai da hakikanin abin da ake bukata a lokaci na sauyin yanayi.

More from this stream

Recomended