
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da shugabannin wasu kasashen Africa ta yamma su uku a fadar Aso Rock dake Abuja.
Shugabannin su ne Patrice Tallon na Jamhuriyar Benin, Umaro Sissoco Embalo na Guinea-Bissau da kuma shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, Muhammad Bazoum.
Shugabannin kasashen uku da suka isa fadar Aso Rock ɗaya bayan ɗaya sun samu tarba daga shugaban kasa, Tinubu a gaban ginin ofishinsa.
Duk da cewa babu wata ajenda da aka bayyana kan taron ana ganin ganawar ta su zata mayar da hankali kan batun tattalin arziki.