
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da suka yi mulki tare a shekarar 1999.
Ganawar da yayi da tsofaffin gwamnonin ta gudana ne a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Babu wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar kan dalilin taron.
Tsofaffin gwamnonin da suka halarci ganawar sun haɗa da James Ibori ( Delta state); Donald Duke (Cross River); Niyi Adebayo (Ekiti); Lucky Igbinedion(Edo); Orji Uzor Kalu( Abia ) da kuma Sam Egwu (Ebonyi).
Sauran su ne Chimaroke Nnamani (Enugu); Ibrahim Saminu Turaki (Jigawa); Adamu Muazu (Bauchi); Obong Victor Attah (Akwa Ibom)’ Olusegun Osoba (Ogun); Bisi Akande (Osun); Ahmad Yerima (Zamfara); Jolly Nyame (Taraba); Attahiru Bafarawa (Sokoto) da kuma Joshua Dariye (Plateau).
A shekarar 1999 Tinubu da tsofaffin gwamnonin an zabe su a matsayin gwamnoni bayan da Najeriya ta dawo tsarin mulkin dimakwaradiya.