Tinubu ya gana da tsofaffin gwamnonin da suka yi mulki tare a 1999.

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da suka yi mulki tare a shekarar 1999.

Ganawar da yayi da tsofaffin gwamnonin ta gudana ne a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Babu wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar kan dalilin taron.

Tsofaffin gwamnonin da suka halarci ganawar sun haÉ—a da James Ibori ( Delta state); Donald Duke (Cross River); Niyi Adebayo (Ekiti); Lucky Igbinedion(Edo); Orji Uzor Kalu( Abia ) da kuma Sam Egwu (Ebonyi).

Sauran su ne Chimaroke Nnamani (Enugu); Ibrahim Saminu Turaki (Jigawa); Adamu Muazu (Bauchi); Obong Victor Attah (Akwa Ibom)’ Olusegun Osoba (Ogun); Bisi Akande (Osun); Ahmad Yerima (Zamfara); Jolly Nyame (Taraba); Attahiru Bafarawa (Sokoto) da kuma Joshua Dariye (Plateau).

A shekarar 1999 Tinubu da tsofaffin gwamnonin an zabe su a matsayin gwamnoni bayan da Najeriya ta dawo tsarin mulkin dimakwaradiya.

More News

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon É—an majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...