Tinubu Ya Gana Da Shugabannin Hukumomin Tsaro

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da shugabannin hukumomin tsaro a fadar Aso Rock dake Abuja.

Babu wata sanarwa da aka fitar kan makasudin taro sai dai ana ganin kiran taron da shugaban kasar yayi baya rasa nasaba da yadda sha’anin tsaro ke cigaba da taɓarɓarewa musamman a yankin birnin tarayya Abuja.

A ranar Lahadi ne masu garkuwa da mutane suka kashe Nabeeha ɗaya daga cikin yan gida mata su shida da aka yi garkuwa dasu a matsayin gargadi ga iyayenta kan yadda suka gaza biyan kuɗin fansar miliyan 60 da aka saka musu.

More from this stream

Recomended