Tinubu ya gana da shugabancin kungiyar CAN

Dantakarar shugaban kasa a jam’iyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya gana da shugabancin kungiyar kiristoci ta CAN a wani kokari na shawo kan kungiyar ta goyi bayan takarar sa.

Kungiyar ta ci alwashin kin marasa masa baya tun bayan da ya zabi Kashim Shettima a matsayin wanda zai masa takarar mataimaki.

A ganawar ta su Tinubu ya bayyana cewa kasancewar yana da mata da kuma yaya dake bin addinin kirista babu yadda za a yi ya nuna wa kiristoci banbanci a gwamnatin da yake son kafawa.

More from this stream

Recomended