
Shugaban kasa, Bola Ahmad ya gana da ɗaya daga cikin manyan ƴan takara da su ka kara da shi a zaɓen 2023, tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a fadar Aso Rock dake Abuja.
Kwankwaso wanda ya zo na huɗu a zaɓen ya yi takara ne a ƙarƙashin jam’iyar NNPP mai kayan marmari.
Shi ne ɗan takarar shugaban kasa na farko da ya kai wa Tinubu ziyara a fadar Aso Rock.
A watan da ya wuce ne mutanen biyu suka yi wata ganawa a birnin Paris na kasar Faransa.