
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da tsohon shugaban shugaban jam’iyar APC, Abdullahi Adamu da kuma tsohon sakataren jam’iyar, Iyiola Omisore a fadar Aso Rock dake Abuja.
Mutanen biyu sun sauka daga kan mukamansu gabanin taron kwamitin zartarwar jam’iyar APC da aka shirya gudanarwa a baya kuma aka dage taron.
Shugaba Tinubu wanda shi ne jagoran jam’iyar baki daya yana da fada aji a cikin jam’iyar APC kuma ana sa ran zai taka muhimmiyar rawa wajen zaɓen sabbin shugabannin jam’iyar.
Babu wata sanarwa kan dalilin ziyarar da suka kai amma ana ganin baya rasa na saba da warware rikicin da ya dabaibaye jam’iyar.