Tinubu ya fara ziyarar aiki ta kwana 3 a Equatorial Guinea

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya isa Malabo babban birnin ƙasar Equatorial Guinea inda zai fara wata ziyarar aiki ta kwanaki uku.

A ranar Talata fadar shugaban ƙasa ta fitar da wata sanarwa dake cewa Tinubu zai ziyarci ƙasar ne bisa gayyatar da shugaban ƙasar Teodoro Mbasogo ya yi masa.

A wata sanarwa ranar Laraba mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya ce Tinubu ya samu tarba daga firaministan ƙasar Manuella Botey.

“Bayan sauka a filin jirgi Tinubu ya samu takaitaccen bikin tarba bayan nan ya wuce zuwa fadar shugaban ƙasa wacce aka fi sani da People Palace Court,” Ngelale ya ce.

A yayin ziyarar Tinubu zai rattaba hannu kan wata yarjejeniyar ƙasa da ƙasa da ta mayar da hankali kan ɓangaren mai da iskar gas da kuma tsaro.

A cikin ƴan rakiyar shugaban ƙasar akwai ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar  da Ekperikpe Ekpo ministan harkokin man fetur bangaren iskar gas da kuma ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo.

Sauran sune, Lateef Fagbemi ministan shari’a, Jamila  Ibrahim ministar matasa da kuma shugaban kamfanin mai na NNPCL, Mele Kyari.

More from this stream

Recomended