Tinubu Ya Bada Umarnin Kamo Wadanda Suka Kai Harin Jihar Filato

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi allawadai da abin da ya kira mummuna da mummuna harin da aka kai kananan hukumomin Bokkos da Barikin Ladi dake jihar Filato inda aka kashe mutane da dama.

Shugaban kasar cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya fitar ya umarci jami’an tsaro da su gaggata isa yankin kana su tabattar an kama wadanda suke da hannu a harin.

Har ila yau shugaban kasar ya bayar da umarni da ayi gaggawar tattarawa tare da kai kayan agaji ga wadanda suka tsira daga harin da kuma kula da lafiyar wadanda suka samu rauni.

A yayin da yake wa gwamnatin jihar Filato da kuma mutanen jihar Filato ta’aziyya shugaban kasar ya bawa yan Najeriya tabbacin cewa wadannan jakadun kisan kai da saka ciwo da jimami baza su tsira daga hukuncin ba.

More from this stream

Recomended