Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya musalta maganganun da ake ta yadawa a gari cewa zai kara aure.
A yan kwanakin nan wasu bayanai suka ɓulla soshiyal midiya dake cewa Tinubu ya shirya angon cewa da amaryarsa yar jihar Katsina.
A wata sanarwa da mataimakin sa kan kafafen yada labarai, Abdulaziz Abdulaziz ya fitar,Tinubu ya bayyana cewa ko kusa babu kanshin gaskiya kan kalaman da ake yadawa.
Abdulaziz ya nemi jama’a su yi watsi da batun domin babu gaskiya a ciki.