Tinubu na kewa aiki ba APC – Wike

Tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce shi yana aiki da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ne ba jam’iya ba.

Da yake magana yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba Wike ya ce shi ba ɗan jam’iyar APC ba ne kuma ba jam’iyar yake wa aiki ba.

Naɗin muƙamin minista da aka yiwa Wike a gwamnatin Tinubu ta jam’iyar ya sa mutane sun bayyana ra’ayi ma bambanta da dama.

Da aka tambaye shi a yayin ganawar kan kasancewarsa mamba a jam’iyar PDP, tsohon gwamnan ya ce har yanzu yana nan a cikin jam’iyar PDP.

Ya ce ya karbi mukamin ne domin ya taimakawa shugaban kasa ba wai jam’iya ba.

More from this stream

Recomended