Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na duba yiyuwar dawo da tallafin mai na wucin gadi a yayin da farashin mai da kuma na dalar Amurka ke cigaba da karuwa.
Wasu majiyoyi dake fadar shugaban kasa sun shedawa jaridar The Cable cewa tabbas ana tattauna yiyuwar yin haka duba da yadda ƴan Najeriya ke cigaba da shiga cikin mawuyacin hali tun bayan cire tallafin.
Tuni ƴan kungiyar kwaɗago suka yi barazanar shiga yajin aikin sai baba ta gani idan har aka samu karin farashin kudin man.