Connect with us

Hausa

Thiago Alcantara ba zai buga wa Liverpool wasa biyu ba

Published

on

Thiago Alcantara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Thiago ya ji rauni a wasan da Liverpool ta doke Crystal Palace 3-0 ranar Asabar a Premier League

Mai buga wasa daga tsakiya a Liverpool, Thiago Alcantara ba zai buga wasa biyu, sakamakon raunin da ya yi.

Mai shekara 30 ya ji rauni ne ranar Asabar a gasar Premier League da Liverpool ta doke Crystal Palace 3-0 a Anfield.

Kungiyar Anfield za ta ziyarci Norwich City a Caraboa Cup ranar Talata, sannan ta ziyarci Brentford ranar Asabar a gasar Premier League.

A minti na 62 Liverpool ta cire Thiago daga wasan ta maye gurbinsa da Naby Keita, wanda shine ya ci kwallo na uku.

Mai tsaron bayan Liverpool, Trent Alexander-Arnold bai buga karawa da Palace ba, ba dai samu zuwa Norwich ba ranar Talata.

Shi kuwa Roberto Firmino ya fara atisaye, bayan da bai buga wa kungiyar karawa uku ba, sakamakon jinya.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending