Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da ci gaban da aka samu wajen farfado da rukunin wutar kasa bayan wata tangardar wutar lantarki da ta faru a ranar Litinin, 14 ga Oktoba, da karfe 6:48 na yamma.
An fara kokarin dawo da wutar nan take, inda tashar wutar Azura ta taka muhimmiyar rawa wajen fara aikin gyaran rukunin wutar.
Duk da cewa an samu ci gaba mai yawa wajen dawo da wutar zuwa karfe 10:24 na safe a ranar Talata, TCN ta fuskanci dan tangarda wanda ya rage gudun aikin na dan wani lokaci.
“Duk da wannan dan tangarda, TCN ta cigaba da aikin farfado da rukunin wutar, wanda yanzu ya kai matakin ci gaba,” in ji kamfanin, yana tabbatar da samuwar wutar lantarki mai yawa ga kusan kashi 90% na tashoshin wutarsa a fadin kasar.
An samu nasarar dawo da wutar a muhimman wurare, ciki har da yankin Abuja da sauran manyan cibiyoyin rabon wuta a fadin kasar.
Abu mafi jan hankali, tashar samar da wutar Ibom Gas ba ta fuskanci matsala ba, tana ci gaba da samar da wuta ga yankunan Kudu maso Kudu, ciki har da Eket, Ekim, Uyo, da tashoshin rarraba wuta na Itu 132kV.