Tanzania: Gwamnati ta musanta bullar Ebola

Ebola


Cutar Ebola ta yi sanadin mutuwar dubban mutane a wasu kasashen Afurka

Gwamnatin kasar Tanzania ta sanar da cewa babu gaskiya a jita-jitar da ake yadawa kan cutar Ebola ta bulla a kasar.

Ministar Lafiyar kasar Mis Ummy Mwalimu, ta shaidawa taron manema labarai cewa sam batun labarin kanzon kurege ne.

A dan tsakanin nan an yi ta yada jita-jitar Ebola da shiga kasar lamarin da ya sanya hankula suka tashi.

Wasu rahotanni na bogi sun ce tuni hukumar lafiya ta duniya WHO ta tura tawagar kwararru Tanzania domin gudanar da bincike, yayin da ofishin jakadancin Amurka ya sanar da jami’ansa su zauna cikin shiri.

An kuma yada shi a shafukan internet, da na sada zumunta.

  • Tanzania ta haramta amfani da Leda
  • Ana cin tarar ‘matan da suka haihu a gida’ a Tanzania

Mis Mwalimu ta ce kasarta a shirye ta ke domin magance duk wata matsalar lafiya da ka iya tasowa, kuma tuni su ma su kayi shirin ko-ta-kwana, musamman a lokacin nan da Ebolar ke kara zama gagarumar matsala a wasu kasashen Afirka.

Ta kara da gargadin jama’a su daina yada labaran karya, musamman a shafukan sada zumunta wanda hakan na tada hankalin gwamnati da jama’a.

Ta ce tun da fari, an fara yada jita-jitar ne sakamakon wasu mutane biyu da aka kebe, da kuma ake zargin suna dauke da cutar.

Amma ta ce bayan ma’aikatar lafiya ta yi musu gwajin jini kamar yadda ya kamata an gano ba sa dauke da cutar Ebola.

More from this stream

Recomended