Tana Kasa Tana Dabo Ministan Tsaro Dan-Ali Da Masarautu

Ana ci gaba da takaddama tsakanin Ministan Tsaro Mansur Dan’ali, da ya zargi wasu sarakunan gargajiya da hannu a mu’amala da ‘yan bindiga masu tada kayar baya a jihar Zamfara,.

Su kuma Sarakunan sun kalubalanci ministan da ya fito karara ya bayyana sarakunan da ake zargi, da kuma zargin jami’an tsaro da kisan jama’ar da basu jiba basu gani ba, a yakin da suke da ‘yan bindiga a jihar.

Yanzu haka sarakunan sun soma fadawa tarkon ‘yan tada kayar bayan a wasu yankuna, kamar a jihar Katsina inda har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, Magajin Garin Daura Musa Umar, yana hannun wasu ‘yan bindiga da suka same shi har gidansa suka yi awon gaba da shi.

A baya-bayan nan kuma a jihar Sokoto, wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a garin Balle, shelkwatar karamar hukumar mulki ta Gudu, inda suka je har gidan basaraken garin mai shekaru 82, Ibrahim Aliyu, suka yi masa kisan gilla, bayan da suka kona ofishin ‘yan sandan garin.

Wani dan rajin kare hakkin bil Adama, kuma shugaban kungiyar Rundunar Adalci a jihar Sokoto, Bashar Altine Isa, yana ganin lamarin da daure kai ainun.

To sai dai mai sharhi akan lamurran yau da kullun, da sha’anin tsaro Bashir Muhammad Achida, yana ganin da akwai sako tattare da sabon salon kai farmaki ga sarakuna.

Wadannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin Najeriya take cewa tana samun nasara, a yaki da take yi da ‘yan tada kayar baya a jihar ta Zamfara da kuma makwabtan jihohi.

More News

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...

Hukumar NDLEA ta lalata sama da tan 300 na miyagun kwayoyi da aka kama a Legas da Ogun

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta yi nasarar lalata kilogiram 304,436 da lita 40,042 na haramtattun abubuwa da...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...