Tambuwal ya yi ganawar gaggawa da alummar garuruwan da aka samu bullar yan bindiga

A wani mataki ndake zama riga-kafi kan matasalar yan bindiga dake neman addabar wasu sassan jihar Sokoto gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal ya yi wata ganawa da mutanen Sabon Garin Liman dake karamar hukumar Wurno.

Ganawar da gwamnan ya yi da su na zuwa ne bayan da aka samu rahoton bullar yan bindiga a yankin.

Tambuwal ya isa garin da tawagar jami’an tsaro da suka hada sojoji, yan sanda da sauran jami’an hukumomin tsaro.

A yayin ziyarar gwamnan ya gargadi yan bindigar da kuma masu basu bayanai da su yi nesa da jihar ko kuma su fuskanci hukunci mai tsauri idan suka shiga hannu.

More from this stream

Recomended