Tambuwal Ya Ayyana Ranar Litinin A Matsayin Hutun Shekarar Musuluncin

0

Gwamnatin jihar Sokoto ta ayyana ranar Litinin a matsayin hutun sabuwar shekarar musulunci.

Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da shi da kansa ya sanyawa hannu.

Tambuwal ya ce ya dauki matakin ne biyo tattaunawa da yayi da, Mai Alfarma Sarkin Musulumi Muhammad Saad Abubakar kan ganin watan Muharram da aka yi.

Ya shawarci mazauna jihar da su sanya a ransu darussan da suke cikin watan kasancewar sa daya daga cikin watanni hudu masu daraja da aka haramta yaki a ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here