Takaddama ta taso kan wani shirin talbijin na ‘cacar halal’ | BBC Hausa

0
Screenshot from Iranian media showing the host of the show

Hakkin mallakar hoto
iSNA

Image caption

Jarumi kuma Mai tallan tufafi Mohammad Reza Golzar na gabatar da shirin Mai Rabo-Ka-Dauka

Gidan talbijin na kasar Iran ya yi dakatarwar wucin gadi ga wani shiri kwatankwacin cacar ‘Dare Daya Allah Kan yi Bature’ bayan korafi daga manyan malaman addini da kuma masu ra’ayin tun iyaye da kakanni.

Jagoran addini a kasar Ayatullah Ali Khamenei ya yi gargadin cewa shirin talbijin din na jefa “al’adar aiki tukuru da kishin neman na-kai” da kasar ke neman karfafa wa gwiwa cikin hatsari.

A yanzu kuma wani jigon malamin Shi’ah ya ba da wata fatawa da ke haramta shirye-shiryen samun garabasa ta hanyar biyan kudi.

Caca dai haramun ce a dokar addinin Musulunci.

Fatawar Ayatullah Nasser Makarem-Shirazi ta fada ne kan shirye-shiryen da ke ba da ladan kudi ga masu kallo da kuma mahalarta.

Makarem-Shirazi ya bayyana su da cewa wani nau’in “caca” ne da kuma “gasar mai rabo-ka-dauka” inda ya nanata cewa duk haramun ne a musulunci.

Shirin, wanda wani jarumin fim kuma mai tallan tufafi Mohammad Reza Golzar ke gabatarwa, yana bai wa ‘yan takara damar cin kudin Iran sama da riyal biliyan daya (kimanin naira miliyan 9) da kuma ‘yan kallo idan sun shiga gasar daga gida ta hanyar wata manhajar intanet.

Kamfanonin labarai sun soki lamirin gidan talbijin din Iran (IRIB) kan “bude gidan cacar halal” ta hanyar gasanni masu salon kale-kale ga ‘yan kallo.

Hakkin mallakar hoto
iSNA

Image caption

Fatawar Malamai ta shafi kudin da ake bayarwa ne a matsayin garabasar da aka ci a shirye-shiryen talbijin din

Gidan talbijin din ya ce ya kaddamar da bincike kan wasu shirye-shiryen da ke gudanar da irin wannan gasa.

Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa za a dakatar da shirin Mai Rabo-Ka-Dauka akalla tsawon mako guda, yayin da manyan jami’an gidan talbijin din kasar suka ce za su sauya masu daukar nauyin shirin.

Shi ma wani shirin Dare Daya Allah Kan Yi Bature, mai suna Five Stars ya fada wa masu bibiyarsa a shafin Instagram cewa ba za a gabatar da shirin wannan makon ba, amma bai yi wani karin bayani ba.

Masu ra’ayin tun iyaye da kakanni sun bukaci daukar kwakkwaran mataki kan abin da suka ce “zubar da kima” ne, har ma sun yi nuni da a kori shugabannin gidajen talbijin din da suka watsa shirin Mai Rabo-Ka-Dauka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here