Sweden na fuskantar hasarar kudi da ƙalubalen tsaro saboda ƙona Alƙur’ani

Hukumomin tsaro a kasar Sweden sun ba da rahoton tabarbarewar yanayin tsaro a kasar, bayan da aka ce an amince da kona kur’ani mai tsarki a kasar.

Wannan hukunci da aka yanke watanni tara da suka gabata, ba wai kawai ya janyo suka daga kasashen duniya ba ne, har ma ya janyo asarar kusan dalar Amurka 200,000 a cewar wani rahoto na baya-bayan nan daga wata kafar yada labarai ta kasar.

Wannan mataki na kona kur’ani mai tsarki da wasu mutane da suka hada da dan siyasar kasar Denmark Rasmus Paludan da dan gudun hijira dan kasar Iraqi Salwan Momika suka aiwatar, ya haifar da gagarumin tasiri na kudi.

An bayar da rahoton cewa, Sweden ta yi asarar krona miliyan 2.2 (daidai da dala 199,300) saboda irin wadannan munanan ayyuka, kamar yadda gidan rediyon Sveriges ya tabbatar.

Abubuwan da ake ta cece-kuce a kan kona kur’ani ya sanya ‘yan sanda sun kara yawan jami’an tsaro da kuma shiga tsakani don tabbatar da tsaro, kamar yadda rahoton da gidan rediyon ya bayyana.

More News

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...