Yayin da magoya bayansa ke yi masa kirari, su kuwa masu adawa da shi na kallon a matsayin bakin-ganga kuma wani mutum mai haɗari da ke tayar da wutar ƙabilanci da kashe-kashe.
A shekarun baya, a yankinsu na kudu maso yammacin Najeriya kaɗai aka san Sunday “Igboho” Adeyemo, amma yanzu ya zama ɗaya daga cikin waɗanda aka fi tattaunawa a kansu – kuma masu raba kan al’umma – a faɗin Najeriya.
Cikin wasu kalaman rura wuta, mutumin da ke sana’ar sayar da motoci ya yi tsamo-tsamo a cikin rikicin ƙabilanci – wato rikici tsakanin Fulani makiyaya da sauran ƙabilu.
Rikici tsakanin manoma da makiyaya game da filayen noma da kuma burtali ya yi sanadiyyar kashe dubban mutane a cikin shekara 20 da suka gabata.
An kambama shi a wani fim
Bayan kashe wani ɗan siyasa a watan da ya wuce, Mista Adeyemo ya ja hankalin duniya bayan ya buƙaci Fulani makiyaya ‘yan arewacin Najeriya su bar yankin kudu maso yamma, inda Yarabawa ke zaune, saboda zargin aikata laifuka.
Sai dai mutumin da ake tunanin yana kare masu rauni, Igboho – wanda ya samo sunansa daga garinsu a Jihar Oyo – ya daɗe yana jawo fitina.
An kambama ɗan shekara 48 din a cikin wani fim da aka yi a shekarun 1990 da harshen Yarabanci, inda aka nuna rikici tsakanin wasu al’umma biyu. Haka nan fim ɗin na cike da tsafe-tsafe da guraye da layu.
A cikin wata fitowa a fim ɗin a lokacin da wasu ƙabilu za su fafata, tauraron fim ɗin mai suna Adeyemo ya zo a kan babur sannan ya ɗauki wata ayaba mai guba kuma ya ci ba tare da wani abu ya same shi ba. Sai kawai ya fito da bindiga ya buɗe wa abokan gabarsa wuta.
Wannan fim ɗin da ire-irensa – ciki har da wanda yake yawo da maciji a wuyansa – ya jawo ana yi masa kallon gagara-badau.
- An haife shi a 1972 a Igboho da ke Jihar Oyo
- Yana sana’ar sayar da motoci sabbi da kuma waɗanda aka yau
- Makaniken babur ne lokacin da yake matashi
- Yana da gidauniya mai sunansa da ke tallafa wa mabuƙata
Adeyemo ya tayar da ƙura a ƙasa baki ɗaya a lokacin da ya yi amfani da ranar bikin ‘yancin kai a watan Oktoba ya yi kira da a ƙirƙiri ƙasar Yarabawa mai zaman kanta, duk da cewa mutane sun tsangwame shi game da shawarar tasa.
Yanzu da yake ƙara zama fitila ga magoya bayansa, an fara ɗaukar ƙorafe-ƙorafensa da mahimmanci.
Maganar mallakar ƙasa ce kan gaba a cikin ƙorafin da yake yi ɗin.
Fulani makiyaya tare da iyalansu kan yi tafiyar kilomita dubbai daga Arewa zuwa Kudu a Najeriya da ma wajen ƙasar aƙalla sau biyu a shekara domin kiwo. Sai dai hakan ya sha jawo rikici tsakaninsu da mutanen yankunan da suke bi, inda ake zarginsu da lalata amfanin gona.
Kazalika, ana zargin wasunsu da aikata garkuwa da mutane domin kuɗin fansa.
Wasu daga cikin masu arziki a Kudu kan ɗauki Fulanin aiki domin kula musu da shanunsu da suke kiwo.
Wani yunƙuri da gwamnnatin Tarayya ta yi a 2019 domin kawo ƙarshen matsalar ta hanyar ƙirƙirar wuraren kiwo bai yi nasara ba, yayin da akasarin gwamnonin Kudu suka ƙi amincewa da shi suna masu zargin Shugaba Buhari da ƙoƙarin mallaka wa ‘yan ƙabilarsa ƙasa.
Rikicin ya ƙara ƙamari a ‘yan shekarun nan sakamakon Fulanin da manoman suna ɗaukar makamai domin kare kansu daga hare-haren da suke kai wa juna.
Kazalika, gwamnonin yankin na kudu maso yamma sun ƙirƙiri wata rundunar tsaro mai suna Amotekun domin su yaƙi matsalar.
Haka nan, an haramta yawon kiwo a dukkanin jiha shida na yankin.
Lamarin ya ƙara rincaɓewa a watan Disamba biyo bayan kisan wani ɗan siyasa a Jihar Oyo mai suna Fatai Aborode.
Adeyemo ya yanke shawarar ɗaukar fansa ta hanyar korar Fulani ba tare da bayar da wata hujjar da ke nuna hannunsu a cikin laifin da kuma sauran kashe-kashen da ake aikatawa.
Bayan wa’adin da ya ba su na kwana bakwai ya cika a watan Janairu, ya jagoranci wani maci a yankin da aka yi kisan, inda aka ƙona gidajen wasu Fulani da suka shafe shekaru a wurin.
‘Jikina kyarma yake idan aka ambaci sunansa’
Abdulkadri Saliu, shi ne shugaban Fulani a yankin wanda aka ƙona gidansa kuma yanzu yake gudun hijira, ya zargi Adeyemo da kunna wutar rikici.
“Nakan ji tsoro duk sanda aka ambaci sunan Igboho,” in ji shi, yana mai cewa bai taɓa ganin tashin hankali kamar haka ba.
Ya ce an kashe ƙaninsa yayin harin.
Adeyemo ya musanta zargin da ake yi masa na haddasa tashin hankali, yana cewa ‘yan sandqa sun goya masa baya tun daga farko har ƙashen lamarin.
Amma fa ya yi tattaki zuwa Yewa na Jihar Ogun domin korar Fulanin daga can ma.
Wasu dandazon matasa ne suka tarɓe shi, inda ya riƙa ziga su da cewa “‘yan daba makiyaya” sun tsira da laifin da suka aikata saboda “saboda makiyaya na kusa da gwamnatin tarayya”.
“Duk wani Bafulatani da ke aikata garkuwa da mutane ya kamata a fito da shi,” a cewarsa.
‘Yan sanda sun ce suna bincike kan lamarin amma sun kasa tabbatarwa ko yana cikin waɗanda ake zargi da tayar da fitina.
Wani ɗan majalisar tarayya Shina Peller ya yabi Adeyemo cikin wani saƙo da ya wallafa a Instagram.
Sai dai wasu ‘yan siyasa daga arewacin Najeriya sun yi Allah-wadai da ayyukan nasa, suna zarginsa da haddasa ƙabilanci da kuma fitar da ‘yan ƙasa daga wuerin zamansu ba bisa doka ba.
Kazalika, wani asusu da aka buɗe mai suna GoFundMe domin tallafa wa ayyukan nasa ya samu naira miliyan 10 cikin ƙasa da kwana ɗaya.
‘Yan Najeriya na da ikon zama a duk inda suke so’
Masu goyon bayan Adeyemo na zargin gwamnatin tarayya da ƙin yin abin da ya kamata wurin dakatar da hare-haren makiyaya a kan mazauna ƙauyuka.
Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom, wanda kafin ‘yan kwanakin nan jiharsa ke kan gaba wurin irin wannan rikici, na ganin cewa lamarin ya ta’azzara ne saboda tausayin da shugaban ƙasa ke nuna wa Fulani makiyaya.
Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu ya faɗa wa BBC cewa ba zai mayar da martani ba game da kalaman gwamnan, yana mai cewa “‘yan Najeriya na da ikon zama a kowane ɓangare na ƙasar”.
Shi ma shahararren marubucin nan ɗan yankin kudu maso yamma, Wole Soyinka, ya soki Buhari kan shurun da ya yi game da ayyukan makiyayan.
“Me suke tsammani daga gare mu tun da yanzu yaƙi ya cim mana? Tabbas za a riƙa samun yunƙurin matasa wanda idan muka zauna jiran gwamnatin tarayya za mu zama bayi a garuruwanmu,” kamar yadda ya faɗa wa BBC.
Ya ce Adeyemo ya mayar da martani ne ta hanyar ya fi kwarewa a kai.