Sojojin sun kwato tarin makamai a hannun Boko Haram

0

Rundunar sojan Najeriya ta sanar da cewa dakarunta sun samu nasarar kwato makamai masu yawa a hannun mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce dakarunta na rundunar Hadin Kai sun samu nasarar kai harin ne da taimakon jiragen yaki daga rundunar sojan sama.

Sanarwa ta kara da cewa an kai farmakin ne a wajen kan titin Wajiroko-Damboa.