Sojojin sun dakatar da wata mata da tayi yunkurin kashe kanta a Lagos

Rundunar sojan Najeriya ta ce sojoji sun hana wata mata mai suna, Francesca Spark kashe kanta bayan da ta yi tsalle ta faɗa ruwa a jihar Lagos.

Olabisi Ayeni, mai magana rundunar sojan Najeriya shiya ta ɗaya shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ranar Litinin.

Ayeni ya ce sojojin Bataliya ta 65 dake aiki a wurin hutarwa manyan sojoji na shiya ta 81 dake Marina su ne suka daƙile yunkurin kisan kan.

Ya ce sojojin sun gano Spark inda suka gaggauta yin amfani da dabarar su ta soja wajen ceto rayuwarta.

Bayan da likitoci suka duba ta an tuntubi danginta inda aka miƙa ta hannun mijinta mai suna, Mr Ovie Spark dake zaune a Awoyaya Lagos.

More from this stream

Recomended