Sojojin Saman Najeriya Na Ci Gaba Da Murkushe ‘Yan Bindigar Zamfara

[ad_1]

A cewar kakakin rundunar sojojin saman Najeriya, Kwamanda Ibikunle Daramola, ganin irin ci gaban da rundunar ke samu nan bada dadewa ba za a kawo karshen duk ayyukan ta’addancin da ‘yan bindigar ke yi a jihar Zamfara.

kamar yadda rundunar ta shaidawa sashen Hausa na Muryar Amurka, wani jirgin saman soji mai liken asiri, ya tattaro bayanan sirri dangane da maboyar ‘yan bindigar a dajin Sabubu, dake karamar hukumar birnin Magaji da kuma dajin Rugu dukkanninsu a jihar ta Zamfara.

Lokacin da jirgin yaki mai saukar ungulu ya kai wa ‘yan bindigar hari a yankin Galadi, dake arewa maso yammacin Zamfara, ya halaka ‘yan bindiga masu yawa, yayin da wasu kalilan suka tsere zuwa dajin Sabubu, inda can dinma ya bisu ya kashesu.

Haka kuma sojojin saman sun hango wasu ‘yan bindiga masu yawan gaske akan Babura dauke da manyam makamai masu sarrafa kansu, yayin da suke tunkarar garin Magaji don kai hari, inda nan take aka bude musu wuta.

‘Karin wasu jiragen yaki guda biyu sun kai wani babban farmaki zuwa dajin Rugu, inda suka ragargaza maboyar makamai da kayayyakin ‘yan bindigar.

A cewar Ibrahim Janyau, dake zama shugaban wata kungiyar fararen hula dake rajin samar da zaman lafiya a jihar ta Zamfara, sun gamsu da irin nasarar da sojojin ke samu, amma ya ce yawan dakarun sunyi kadan, duba da yadda yanzu aika aikar ke daukar wani sabon salo, ganin cewa lokacin da sojojin ke fafatawa a arewacin jihar sai wasu kuma su kaddamar da farmaki a kudanci ko gabashin jihar.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

[ad_2]

More News

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...

AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.An bayyana hakan...

Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a...